Neman lamunin kudi ta hanyar jinginar mota yana zuwa da tambayoyi daban-daban game da tsaron mota, tsarin kwangila, da saurin samun kudi. Ga amsoshin tambayoyin da abokan cinikayya ke yawan tambaya a ALHERI LENDING COMPANY LTD.
1. Shin zan iya samun lamuni ba tare da mai tsaya mini ba?
E. Motarka ita ce tabbacin lamunin. Ba ma buqatar wani mutum daban ya tsaya muku.
2. Yaya ake ajiye motata yayin da nake bin bashi?
Ana ajiye motarku a garajinmu mai tsaro na sa’o’i 24/7. Motarku za ta kasance a ajiye cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ya tuka ta ba.
3. Shin akwai kudaden boye na ba-zata?
A’a. Muna aiki ne da tsarin gaskiya. Dukkan kudaden ana bayyana su sarai a kwangilar kafin sanya hannu ba tare da kudaden boye ba.
4. Wadanne takardu ake buqata don neman lamuni?
Kuna buqatar asalin Takardar Mallakar Mota (POC), katin shaida mai aiki (NIN ko Fasiye), da makullin mota.
5. Yaushe kudi ke shiga asusun banki?
Bayan an gama duba mota da tabbatar da takardu, kudi na shiga asusun bankinku cikin mintuna 30.
Kuna da Tambayoyi Game da Darajar Motarku?
Sami kimanta mota kyauta nan take a WhatsApp daga ƙungiyarmu.